1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure sun nitse a ruwan Libiya

February 16, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta ce bakin haure da dama ne suka mutu sakamakon kifewar da kwale-kwalensu ya yi a gabar ruwan Libiya.

https://p.dw.com/p/4NY43
Ocean Viking I Migranten aus dem Mittelmeer gerettet
Hoto: Vincenzo Circosta/AA/picture alliance

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin bakin haure 80 ne cikin kwale-kwalen da ya taso daga yankin Qasr al-Akhyar da ke gabashin birnin Tripoli da nufin zuwa nahiyar Turai suka nitse. Kawo yanzu dai hukumar ta ce an gano gawawwaki 11, sai dai ana zargin sauran fiye da 70 sun mutu yayin da har yanzu ake ci gaba da nemansu.

Wasu bakwai da suka tsallake rijiya da baya kana suka sami damar komawa gabar ruwan Libiya na cikin mawuyacin hali a gadon asibiti. Alkaluma Hukumar kula da kaurar jama'a IOM sun yi nuni da cewa, hatsarin na wannan lokaci ya kawo adadin wadanda suka mutu a Bahar Rum a bana sun kai mutum 130, inda ta bayyana shi a matsayin abun da ba za a lamunce ba.

Ko a ranar Talatar da ta gabata, masu gadin gabar ruwan sun ceto wasu bakin haure 84 daga wani kwale-kwale cunkushe da jama'a a kusa da gabar ruwan Libiya wanda 58 da cikinsu kananan yara ne. IOM ta ce a bara, kimanin bakin haure dubu 1500 ne suka mutu a hanyar da ke zama tamkar siradi a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai domin samun rayuwa mai inganci.