1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Azerbaijan ta yi watsi da taro da Armenia

Abdullahi Tanko Bala
October 4, 2023

Kafofin yada labaran gwamnatin Azerbaijan sun ruwaito cewa shugaban kasar Ilham Aliyev ba zai halarci tattaunawa da Firaministan Armenia Nikol Pashinyan ba.

https://p.dw.com/p/4X7VC
Ilham Aliyev da Nikol Pashinyan da kuma Charles Michel
Ilham Aliyev da Nikol Pashinyan da kuma Charles MichelHoto: Dursun Aydemir/AA/picture alliance

An gayyaci Aliyev domin halartar tattaunawar ta bangarori biyar da kungiyyar tarayyar Turai ta shiga tsakani wanda aka tsara za a yi a Granada, kasar Spain.

An shirya shugabannin kasashen Jamus da Faransa da kuma shugaban majalisar tarayyar Turai Charles MIchel za su halarci taron.

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne akan makomar yankin Nagorno-Karabach, tsohon yankin yan kabilar Armenia da ke cikin Azerbaijan, yankin da Azerbaijan ta kwace a artabun da suka yi a ranar 19 ga watan Satumba wanda ya jawo gagarumin kaurar jama'a da kuma zargin kokarin kakkabe yan kabilar Armenia daga doron kasa.

Firaministan Armeniya Pashinyan ya ce  duk da haka ya kudiri aniyar zuwa Spain domin halartar taron kolin na kungiyar tarayyar Turai, yana mai cewa abin kunya ne janyewar da Aliyev ya yi na kin halartar taron.