1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta yi tir da kalaman Shugaba Jammeh

December 10, 2016

Shugabar hukumar Tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma ta bukaci shugaba Yahyah Jammeh ya mika mulki cikin ruwan sanyi zuwa ga sabon shugaban kasar ta Gambiya.

https://p.dw.com/p/2U4Px
AU Präsidentin Nkosazana Dlamini-Zuma Archiv 16.07.2012
Shugabar Hukumar Tarayyar Afirka AU Nkosazana Dlamini-ZumaHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Kungiyar Tarayyar Afirka AU  ta yi kira ga Shugaba Yahya Jammeh da ya mutunta sakamakon zaben shugaban kasar da ya amince da shi tun da fari kafin daga bisani ya sauya ra'ayinsa. Shugabar hukumar ta Tarayyar Afirka Nkosazana Dlamini-Zuma ta bukaci shugaban da ya mika mulki cikin ruwan sanyi zuwa ga sabon shugaban kasar ta Gambiya kamar yadda ya ce zai yi a baya.

 

Jammeh dai da ya amince da sakamakon zaben na ranar daya ga watan Disamba a ranar Jumma'a ya ce bincike ya gano kura-kurai a zaben kasar dan haka hukumar zaben kasar ta yi kuskure, abin da ya sanya ba zai mika kai ga dan adawarsa Adama Barrow ba. Zuma dai ta ce sakamakon zaben na Gambiya shi ne hakikanin abin da 'yan Gambiya suka zaba don haka Shugaba Jammeh ba shi da ta cewa. Ta ce dukkanin bangarorin biyu su mutunta doka  sannan kwamitin sulhu na kungiyar ta AU zai gaggauta zama kan batun.