1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

AU ta yi fatan nasara ga gwamnatin Diomaye na Senegal

March 29, 2024

Kungiyar tarayyar Afrika ta taya murna ga zababben shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye kan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasa, inda ta yi masa fatan samun ci gaba mai ma'ana a kasar ta yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/4eFGk
Shedikwatar kungiyar tarayyar Afrika AU a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Shedikwatar kungiyar tarayyar Afrika AU a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.Hoto: Solomon Muchie/DW

Sakon taya murnar AU na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar mai barin gado Macky Sall ya karbi bakuncin shugaban kasar mai jiran gado Bassirou Diomaye Faye da madugun adawa Ousmane SONKO a fadar gwamnatin Dakar.

Karin bayani: 'Yan takarar shugaban kasa a Senegal sun kaddamar da yakin zabe 

Shugabannin sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi makomar ci gaban kasar ta Senegal tare da cimma matsaya kan batun shirye-shiryen mika mulki da ake sa rai a ranar 2 ga watan Afrilun wannan shekara.

Karin bayani:  Senegal: Sonko da Diomaye sun shaki iskar 'yanci

Diomaye Faye wanda bai taba rike mukamin siyasa ba shi ne shugaba na biyar da zai mulki kasar tun bayan samun 'yancin kasar tun daga lokacin Leopold Sedar Senghor da Abdou Diouf da Abdoulaye Wade sai kuma Macky Sall mai barin gado.