1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haïti: Annobar kwalara na daukar rayukan jama'a

Abdoulaye Mamane Amadou Zainab Moh' Abubakar
October 19, 2022

Hukumomin lafiya a kasar Haïti sun bayyana karuwar masu kamuwa da cutar Kwalara a daidai lokacin da kasar ke fama da tarin rikice-rikice

https://p.dw.com/p/4INRz
Haiti nach Hurrikan Matthew - Krankenhaus Cholera Behandlung
Hoto: Reuters/A.M. Casares

Mutane 222 sun sake kamuwa da annobar Kwalara da ta barke a baya-bayan nan a kasar Haïti kamar yadda wasu alkaluman hukumomin lafiyar kasar suka zayyana.

Rahoton da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar ya bayyana cewa fursunoni 14 a gidan yarin birnin Port-au-Prince sun mutu, adadin da ya kara alkaluman mamatan ya zuwa yanzu a kasar da ke fama da matsaloli barkatai ciki har da na rashin tsaro.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna matukar damuwa kan halin da kasar ta fada a ciki, yana mai bayyana shi a matsayin mai daukar hankali.