1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana farautar Hama bayan boren zaben Nijar

Gazali Abdou Tasawa MAB
February 25, 2021

Mahukuntan Nijar sun kame Janar Moumouni Boureima a yayin da ake farautar madugun adawan kasar Malam Hama Amadou wanda ya yi batan dabo. Wannan ya biyo bayan tarzomar bayan zabe inda aka samu asarar rai da ta dukiya. 

https://p.dw.com/p/3pvLj
Niger Wahlen Hama Amadou
Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Wata majiyar tsaro mai tushe wacce ta bukaci a sakaye sunanta ta kwarmata wa DW cewa lalle an kame Janar Moumouni Boureima mai ritaya, wanda yanzu haka ake tsare da shi a ofishin 'yan sanda farfaren kaya inda ake yi masa tambayoyi. Ko da shi ke hukumomi ba su yi bayanin dalilan kama tsohon Janar ba wanda ya rikide zuwa dan siyasa a karkashin inuwar jam’iyyar Lumana Afrika ba, amma wasu na danganta lamarin da kalaman tunzuri da ake zargin janar din ya furta a wasu tarukan gangami a lokacin yakin neman zabe.

Sai dai a yayin da wasu 'yan Nijar ke ganin kamun Janar din zai zafafa yanayin siyasar kasar, wasu na ganin bai fi karfin doka ba. Malam SAMNA na kawancen kungiyoyin farar hula na Convergeance Citoyen pour la Démocratie na daga cikin masu irin wannan ra’ayi.

Bildkombo Niger | Mohamed Bazoum und Mahamane Ousmane
Fafatawar Bazoum da Ousmane ta bar baya da kura a Nijar

Bayan kamun Janar din da magoya bayan 'yan adawa sama da 200 da aka kama a lokacin zanga-zangar, yanzu haka jami’an tsaro sun shiga farautar madugun adawa Malam Hama Amadou tsohon dan takarar jam’iyyar Lumana. Amma ya zuwa yanzu ya yi batan dabo. Sai dai Moustapha Kadi na kungiyar kare hakkin dan Adam ta CODAE na ganin kame-kame 'yan siyasa ba shi ne mafita ba.

 Akwai bukatar yayyafa ruwan sanyi a cewar Nassirou Seidu

Tarzomar bayan zabe da ta barke a birnin Yamai ta yi sanadiyyar mutuwar wani jami’i daga cikin masu tsaron lafiyar shugaban jam’iyyar MNSD NASARA Alhaji Seini Omar. Bayanai na nuni da cewa jami’in ya rasu bayan da wani daga cikin masu zanga-zangar bayan zaben ya harbe shi da bindiga.Kuma Malam Nassirou Seidu shugaban kungiyar muryar talakka na ganin cewa akwai bukatar sanya bakin shugaban kasa da na 'yan takarar biyu wajen shawo kan matsalar.

Niger Protest gegen Ergebnis der Präsidentschaftswahl
An samu asarar rai da dukiya a boren bayan zaben Nijar

Ko da shi ke kurar zanga-zangar da kone-konen ta lufa a tsakiyar birnin Yamai, masu zanga-zangar na ci gabada gudanar da ita a wasu unguwannin kewayen birnin Yamai inda suka banka wuta a gidan Moussa Kaka wakilin gidan rediyon RFI a birnin Yamai.