1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da barin wuta a Sudan

April 30, 2023

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta gaza yin tasiri a Sudan yayin da aka shiga mako na uku na gwabzawa tsakanin sojoji masu biyyaya ga janar Abdel Fattah al-Burhane da dakarun RSF da janar Mohamed Hamdane Daglo ke jagoranta.

https://p.dw.com/p/4QiuD
Hoto: Mohamed Nureldin Abdallah/REUTERS

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tir da yadda manyan hafsan sojan Sudan suka bijire wa kiraye-kirayen tsagaita buda wuta, yayin da yakin ya kama hanyar daidaita kasar da dama ba ta mike ba daga tsohon rikicin Darfur.

Kawo yanzu rikicin da ya barke a ranar 15 ga watan Afirilu ya yi ajalin mutane sama da 500 tare da jikkatar wasu gwammai baya ga tilasta wa fararen hula sama da dubu 75 gudu daga kasar i zuwa kasashen chadi da Masar da Habasha da kuma Sudan ta Kudu yayin da kasashen duniya ke ci gaba da kwashe mutanensu.

A jiya Asabar shugaban Suban ta Kudu Salva Kiir wanda a baya ya taka muhinmiyar rawa wajen daidaituwar lamura a Sudan lokacin barkewar yakin Darfur, ya kira manyan hafsoshi sojan da ke kokawar iko da su yi ganawar keke da keke don dinke barakar da ta kunno kai a tsakaninsu ba tare da wata-wata ba.