1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa mutane hukuncin kisa a Iran

July 8, 2023

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane biyu da aka kama da laifin kai hari a wurin ibadar nan mai tarihi na 'yan Shi'a Chah-Cheragh da ke Kundancin kasar.

https://p.dw.com/p/4TcUU
Irin wuraren da ake zartar da hukuncin rataya a Iran
Hoton guda daga cikin wuraren da ake zartar wa masu laifi hukuncin rataya Hoto: Christoph Hardt/Geisler-Fotopress/picture alliance

Kafar yada labaran kasar mallakar gwamnati ta ruwaito cewar an rataye mutane biyu a gaban bainar jama'a a wani titi da ke birnin Chiraz bayan tabbatar ma su da laifin harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 a watan Oktoban shekarar 2022.

Wurin ibadar na Chah-Cheragh da mutanen suka kai wa harin a bara, na daya daga cikin hubbare masu matukar daraja ga mabiya mazhabar Shi'a.

Iran dai na a sahun farko na daidaikun kasashen duniya da har yanzu suke zartar da hukuncin kisa duk da irin gwagwarmayar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke yi don ganin an kawo karshen wannan al'ada.