1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsaurara tsaro bayan dan sanda ya aikata kisa a Faransa

June 30, 2023

Kisan wani matashin dan Afirka dan kasa da shekaru 20, ya janyo zanga-zanga a manyan biranen Faransa da ma kasar Beljiyam. 'Yan sandan dai sun nemi afuwa.

https://p.dw.com/p/4TFzV
Hoto: Gonzalo Fuentes/REUTERS

Akalla jami'an 'yan sanda dubu 40 ne gwamnati a Faransa ta baza a fadin kasar, inda a birnin Paris kadai bayanai ke cewa an girke jami'an su dubu biyar, bayan rikicin da ya barke mai nasaba da mutuwar wani matashi dan asalin arewacin Afirka da wani dan sanda ya yi.

Mutuwar matashin dan shekara 17, ya janyo zanga-zanga a manyan biranen Faransar da ma wasu kasashe makwabta irin su Belgium, abin ma da ya sanya shugaban Faransa Emmanuel Macron ganawa da wasu kusoshin gwamnati a jiya Alhamis.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai Shugaban na Faransa ya ce mutane sun yi ta afka wa ofisoshin 'yan sanda da gine-ginen gwamnati gami da makarantu hare-hare, abin da ya ce ba daidai ba ne.

Shugaba Macron ya kuma yi kalaman sukar dan sandan da ya harbe matashin, yana mai cewa laifi ne da ba za a yafe ba.

Dan sandan dai ya harbe matashin ne a lokacin da yake kokarin tserewa bayan an nemi takardun da za su nuna ko wane ne shi.

Dan sandan da ya aikata kisan, ya nemi afuwar iyayen matashin da ke cikin hali na kaduwa.