1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal:An tsare Ousmane Sonko a gidan yari

Abdullahi Tanko Bala
July 31, 2023

Hukumomi a kasar Senegal sun tsare Jagoran adawa Ousmane Sonko a gidan yari a cewar lauyansa. Ana zargin Sonko da tada zaune tsaye da hada baki wajen aikata muggan laifuka da kuma wasu tuhume-tuhume da ya musanta.

https://p.dw.com/p/4Ubpt
Ousmane Sonko
Madugun adawa a Senegal Ousmane SonkoHoto: Fatma Esma Arslan/AA/picture alliance

An dai kama madugun adawar ne bayan wani artabu da jami'an tsaro a kofar gidansa.

Masu gabatar da kara sun ce laifukan da ake tuhumarsa da su sun biyo bayan kalaman da ya furta ne da taruka da ya gudanar da kuma wasu abubuwan da suka faru tun shekarar 2021.

Dan adawar wanda ya yi kaurin suna wajen sukar shugaban kasa Macky Sall ya ci gaba da yajin cin abinci kwana guda bayan kama shi.

Ministan cikin gida na kasar Senegal ya ce an soke Jam'iyyar Pastef ta Sonko sakamakon yawan kiran da ya ke yi na tunzura jama'a su yi bore abin da ya kai ga haifar da ta'asa da kuma hasarar rayuka.

Ana dai fargabar matakin na iya haifar da sabon tashin hankali a fadin kasar ta yammacin Afirka