1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tarwatsa masu neman jinsi daya a Istanbul

Ramatu Garba Baba MAB
June 30, 2019

'Yan sanda sun tarwatsa faretin masu mu'amala ta jinsi daya a Turkiya. Babu doka kan masu mu'amala da jinsi daya a kasar, sai dai suna fuskantar kyama da musgunawa daga jama'a, lamarin da suka ce sam bai dace ba.

https://p.dw.com/p/3LMks
Türkei Istanbul Polizei geht gegen LGBT Aktivisten vor
Hoto: Reuters/M. Sezer

'Yan sanda a kasar Turkiya sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa dandanzon 'yan rajin kare muradun masu mu'amala ta jinsa daya da suka gudanar da zanga-zanga a dandalin Taksim a wannan Lahadi. Rahotannin sun ce jami'an 'yan sandan sun yi amfani da harsasan roba da hayaki mai sa kwalla don tarwatsa masu boren da suka bijirewar umarnin gwamnati.

Gangamin na zuwa ne a daidai lokacin da sauran masu fafutukar auren jinsi na kasashe dabam-dabam ke gudanar da gangaminsu wajen neman a sakar musu marar auren jinsin. Duk da cewa babu wani takamaimiyar doka kan masu mu'amala ta jinsi daya a kasar, sai dai suna fuskantar kyama da musgunawa daga jama'a, lamarin da suka ce sam bai dace ba.