1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kama wani Pastor da kashe mabiyansa a Kenya

Abdullahi Tanko Bala
April 27, 2023

Ministan cikin gida na kasar Kenya ya ce za a gurfanar da daya daga cikin manyan limaman coci a kasar bisa zargin kisan mabiyansa da dama.

https://p.dw.com/p/4QeGn
Polizisten eskortieren Ezekiel Ombok Odero im Polizeipräsidium in Mombasa
Hoto: Stringer/REUTERS

An dai kama shugaban cocin New Life Prayer Center Ezekiel Odero inda aka tafi da shi zuwa Mombasa kuma ana shirin gurfanar da shi a gaban kotu a cewar ministan cikin gidan na Kenya Kithure Kindiki a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa a halin da ake ciki an rufe cocin kuma mutane kimanin 100 da aka yi wa kawanya a ciki an kwashe su za  kuma a bukaci su bayar da bayanai.

Kama Odero ya zo daidai wani bincike da jami'an tsaro ke yi a kan Paul Mackenzie Nthenge shugaban wani gungu da ake zargi da mutuwar mutane 98 mabiya cocinsa.

Sai dai 'yan sanda basu baiyana ko laifukan biyu suna da dangantaka da juna ba.