1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake bude iyakar Sabiya da Kosovo

Abdullahi Tanko Bala
December 29, 2022

An bude babbar mashigar kan iyaka tsakanin Sabiya da Kosovo inda 'yan kabilar Sabiya suka cire shingayen da suka sanya a yankin arewacin kasar da ake zaman dar dar wanda ya ja hankalin kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/4LYZX
Mitrovica | Kosovo
Hoto: Bojan Slavkovic/picture allliance/dpa

An dai fara da janye shingaye a kan iyakar da ke bangaren Sabiya a kusa da garin Mitrovica a yankin Kosovo tare da kawar da gomman manyan motocin dakon kaya da suka rufe hanyoyi.

Shugaban kasar Sabiya Aleksander Vucic da 'yan sandan Kososvo sun sanar da bude iyakokin bayan kungiyar tarayyar Turai da Amirka sun bukaci gaggauta kwantar da hankula da kuma kai zuciya nesa a tsakanin bangarorin biyu.

Kosovo ta balle daga Sabiya a shekarar 2008 bayan mummunan yakin da suka gwabza a shekarun 1990 wanda ya jawo hasarar rayukan dubban jama'a.