1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An mika daliban Kuriga da aka ceto ga iyayensu

March 29, 2024

A karshe gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya, ta mika dalibai 137 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su ga iyayensu. Iyayen sun yi farin ciki matuka.

https://p.dw.com/p/4eFkc
Wasu daliban makarantar Kuriga da aka kubutar a Kaduna
Wasu daliban makarantar Kuriga da aka ceto a KadunaHoto: Chinedu Asadu/AP Photo/picture alliance

Daukacin a'lummar kauyen Kuriga ne da ke a kaduna a Najeriya ne suka yi  tururuwa wajen tarbar daliban makarantar 137 da 'yan bindiga suka sace, inda iyaye da sauran dangi suka cika makarantar da murnan ganin ‘ya'yansu bayan shafe makwanni uku da rabuwa da su.

Daruruwar iyayen yara daliban makarantar kauyen na Kuriga sun kasance baki har kunne saboda murna sake hada ido da su, bayan gwamnati ta kai su ga iyayen, kamar dai yadda wani mahaifin wata dalibar da aka sako Malam jibrin Gwadabe Kuriga ya tabbatar.

Iyayen, wasu ma da ke da 'ya'yan da suka kai 10 sun yaba wa gwamnati da abin da suka kira kokarin gwamnati na ceto su ba tare da rasa ko da guda daga cikin su ko ma samun rauni ba.

Wasu daga cikin iyayen daliban Kuriga a Kaduna
Wasu daga cikin iyayen daliban Kuriga a KadunaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Sai dai mahaifin Malamin daliban da aka tabbtar da mutuwar a lokacin da aka yi garkuwa da sun, ya nuna bukatar gwamnati ta dauki nauyin karatun abin da ya bari a baya wato 'ya'ya shida da suke a raye.

Mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa ce dai ta jagoranci ayarin da ya maida wadannan dalibai ga iyayen nasu a Kuriga. Ta kuma taya su jajen abin da ya faru.

Tuni ma dai gwamnatin jihar da ke arewacin Najeriyar, ta kafa wata runduna ta tsaro a kauyen na Kuriga a inda wannan iftila'in ya faru.
Kungiyoyi kuma na ci gaba da kiraye-kirayen hukumomi su kara kaimi domin ceto sauran mutane da ma kananan yara da ke ci gaba da kasancewa a hannun 'yan bindigar daji a sassan arewacin Najeriyar a halin yanzu.