1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

'Yan gudun hijira sun koma a gida

Abdoulaye Mamane Amadou
June 21, 2021

Kusan 'yan gudun hijira 6000 sun koma a gida shekaru bayan da suka kaurace sakamakon hare-haren 'yan Boko Haram a yankin Diffa da ke Kudu maso gabashin Nijar.

https://p.dw.com/p/3vHoK
Symbolbild Nigeria Bama Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

Hukumomin kasar dai sun bayyana cewa matakin komawar na radin kai zai shafi fiye da 'yan gudun hijira dubu 1000, da suka baro garuruwansu da ke daf da yankin Tafkin Chadi, don samun mafaka a manyan biranen da basu da kamarin hare-haren 'yan Boko Haram. Ko a karshen makon jiya kimanin mutun dubu 5.935 ne aka yi jigilar komawarsu a Baroua, wani kauyen a kusa da makwabciyar kasar Najeriya, da kuma ya tarwatse sakamakon kamarin hare-haren 'yan ta'adda.

Kafar talabijin din kasar ta nuno mutane shake a cikin motoci na komawa, inda mahukunta suka raka su da abinci, biyo bayan samun saukin hare-haren mayakan da suka addabi yankin tun a shekarar 2015.