1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe gomman mayakan al-Shabaab

November 23, 2022

Gwamnatin kasar Somaliya ta ce, kimanin mayakan al-Shabab 49 dakarunta suka kashe yayin wani samame da aka kai yankin Lower Shabelle a kasar.

https://p.dw.com/p/4JyRo
Dakarun kasar Somaliya
Hoto: Sadak Mohamed/AA/picture alliance

A cikin sanarwar da ma'aikatar yada labarai ta kasar ta fitar, ta ce dakarun Somaliyan tare da hadin gwiwar dakarun kasa da kasa sun lalata tarin ababen hawan mayakan da kuma makamai a kauyen Bulo-Madni da ke yankin. Wasu shaidun gani da ido sun sanar da cewa, sun ji karar ababen fashewa a arewa maso yammacin birnin Magadishu, sai dai ba su da tabbaci kan adadin wadanda suka mutu.

Har yanzu, kungiyar al-Shabaab ba ta mayar da martani kan harin ba. A baya-bayan nan dai, dakarun sojan Somaliya tare da hadin gwiwar sojojin hadaka na kungiyar Tarayyar Afirka na samun galaba kan mayakan na al-Shabaab da ke kai hare-hare a manyan wurare a kasar. Ko a watan Octoban da ya gabata kungiyar ta al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin bam da ya kashe a kalla mutane 120 a babban birnin kasar Magadishu.