1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kasa cimma matsaya a taron G20

February 26, 2023

Ministocin kudi na kasashe masu karfin masana'antu na G20 sun kammala taronsu na shekara-shekara a birnin Bangalo na kasar Indiya ba tare da cimma matsaya guda ba.

https://p.dw.com/p/4NzUf
Taron ministocin kudi na kasashen G20 a kasar IndiyaHoto: India's Press Information Bureau/via REUTERS

Taron ya yi nazari ne kan samar da hanyoyi kubutar da kasashen 20 daga tarnakin da tattalilin arzikin duniya ke fuskanta sakamakon yakin Rasha da Ukraine da kuma hauhawar farashin kaya a kasuwannin duniya. Sai dai sabanin ra'ayi da aka samu da kasar Chaina kan yankin Rasha da Ukraine ya sa aka watse baram-baram.

kanfanin dillancin labarun Faransa AFP ya ruwaito daya daga cikin ministocin da suka halarci taron na cewa har kawo yanzu kasar Chaina ta ki numa matsayinta karara kan mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine. Hasali ma ita ke dafa wa Rashar baya wajen jure wa takunkuman karya tattalin arziki da kasashen Yamma suka kakaba mata.

Sai dai a daya gefe, taron na tsawon kwanai biyu ta tabo wasu batutuwa da dama ciki har da maganar yafe wa kasashe matalauta bashin da ake binsu.