1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da kisan kare dangi kan Yahudawa

Ramatu Garba Baba
January 27, 2023

A ranar 27 ga watan Janairu ta kowacce shekara ake gudanar da bikin tunawa da kisan kare dangi da gwamnatin 'yan Nazi a Jamus ta yi wa Yahudawa.

https://p.dw.com/p/4Mn2w
Bikin tunawa da kisan kare dangi a Jamus
Bikin tunawa da kisan kare dangi a JamusHoto: Artur Widak/AA/picture alliance

A yayin da Jamus ke taron tuni da kawo karshen gwamnatin 'yan Nazi, kasar ta mayar da hankali a kan wadanda aka gallazawa azaba saboda sun kasance masu ra'ayin neman jinsi, an gano yadda yawancin wadanda aka yi wa nau'ukan cin zarafin suka rasa rayukansu a wancan lokacin.

Wannan shi ne karon farko da ake damawa da 'yan Kungiyar ta LGBTQ  a taron da aka kwashi shekara da shekaru ana yi, kan nasarar kawo karshen bala'in da jam'iyyar ta 'yan Nazi ta jefa duniya a karkashin mulkin Adolph Hitler.

Yahudawa kimanin miliyan shida gwamnatin Hitler ta hallaka a yayin yakin da ya faru a tsakanin Jamus da sauran kasashen duniya, daga cikinsu akwai kananan yara da mata. A ranar 27 ga watan Janairu ta kowacce shekara ake gudanar da bikin tunawa da kisan kare dangi da gwamnatin 'yan Nazi a Jamus