1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An lafta wa Rasha karin takunkumai

Ramatu Garba Baba
May 21, 2023

Shugabanin kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki, sun kammala taronsu da jaddada goyon baya ga kasar Ukraine da Rasha ke mamaya.

https://p.dw.com/p/4RdeZ
Taron kasashen G7 a Japan
Taron kasashen G7 a JapanHoto: (Kyodo News/AP)/picture alliance

Shugabanin kasashen duniya mafiya karfin tattalin arziki na G7, sun kammala taronsu na kwanaki uku a Japan da jaddada goyon baya ga kasar Ukraine a yayin da suka aika da sako da kakkausar murya ga Rasha da Chaina. 

Shugabannin kungiyar, sun dauki tsauraran matakai na bai daya a kan kasar Chaina duk kuwa da irin muhimmancin kasar mai karfin tattalin arziki tare da aza sabbin takunkuman karya tattalin arziki akan Rasha, takunkuman da suka hada da katse duk wasu hanyoyi da ta ke samun kayayyakin sojoji da dakile hanyoyin da Rasha ke samun kudaden shiga.