1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da matatar man Dangote a Najeriya

May 22, 2023

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya kaddamar da matatar man fetur ta Dangote a Ijebu Lekki a birnin Legas, matatar da ke iya sama wa sama da mutum dubu 100 aikin yi.

https://p.dw.com/p/4Rg2N
Hoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Akalla dai wannan matatar man fetur ta Lakume dalar Amurka kusan miliyan dubu 19 bikin da aka gudanar a wannan Litinin tare da goyan baya na shugabannin kasashen Afirka hudu, Shugaba Muhammadu Buhari dai a cike yake da murnar cewa an fara a lokacinsa kuma an kammala a daidai lokacin da zai sauka daga karagar mulkin kasar.

Ita dai wannan matata za ta rika samar da gangar man fetur akalla dubu 650 a kowace rana kuma alkaluma sun tabbatar da cewa ta ninka unguwar Victoria Island, unguwa mafi daraja da fadi a Legos har sau ukku. Bugu da kari matatar za ta samar da aikin yi ga jama‘a kusan dubu 100. Najeriya dai kasa ce da ta fi kowace kasa a nahiyar Afirka yawan albarkatun man fetur in aka dauke kasar Libiya

A yayin kaddamar da wannan matata ta Dangote, Shugaba Buhari kira ya yi ga sabuwar gwamnati mai kamawa da ta dauki irin wannan salon na hadin gwiwa da kamfanoni domin ci gaba da habaka fannin tatalin arzikin kasar musamman ta fannin batutuwan da ke da nasaba da samar da hanyoyi da hasken wutar lantarki da sauransu.

Symbolbild | Nigeria Gaspipeline
Hoto: Florian Plaucheur/AFP/Getty Images

To sai dai bayan da  gwamnan babban  bankin Najeriya Mr. Godwin Emiefele ya tashi domin bayani, ya ce tun a baya kasashen duniya ba su yarda cewa wannan mutum daya ne zai iya rungumar aradu da ka ba kamar Dangote sai ga shi hakan ta tabbata.

Mai masaukin baki gomna jihar Legas Babajide Sanwolu cewa ya yi shugabanci na bukatar hangen nesa don cimma manufar da aka sanya a gaba.  

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum na daya daga cikin shugabannin da suka shigo Najeriyar kuma ya jinjina wa shugaban kasa da duk wadanda suka tallafa wa Dangote ya cimma wannan manufa domin ta Afirka ce baki daya musamman a yammaci da sahara. Shugaban Kasashen Ghana da Togo da Senegal da Nijar, su ne suka sami halartar wannan gagarumin biki a kwaryar Legas.))