1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Fara jigilar fararen hula

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 9, 2021

A karon farko tun bayan kammala ficewar dakarun kasashen waje daga Afghanistan, jirgin jigilar fararen hula ya fara tashi daga Kabul.

https://p.dw.com/p/408Uu
Ziviler Evakuierungsflug aus Afghanistan | Landung in Doha
Jirage sun fara jigilar fararen hula 'yan kasashen waje daga KabulHoto: Karim Jaafar/AFP

Rahotanni sun nunar da cewa a yau Alhamis jirgin saman Qatar-Airways ya tashi da mutane sama da 200 zuwa Doha fadar gwamnatin Katar din.  Cikin wadanda aka samu nasarar kwashewa a jirgin farkon, akwai 'yan kasashen Jamus da Amirka da Kanada da Birtaniya da Italiya da Holland da kuma Ukraine. Ana sa ran a Jumma'ar wannan makon, wani jirgin dauke da fararen hular 'yan kasashen waje zai sake tashi daga Afghanistan din. Jakadan musamman na Katar a Afghanistan din, Mutlak al-Kahtani  ya bayyana cewa, filin jiragen saman na birnin Kabul ya koma aiki ka'in da na'in. Kasashen Katar da Turkiyya dai, na aiki kafada da kafada, domin ganin al'amura sun koma yadda suke a filin jiragen samana na birnin na Kabul.