1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bazoum na kan gaba da kuri'u a zaben Nijar

February 22, 2021

Hukumar zabe ta CENI a Jamhuriyar Nijar ta fara sanar da sakamakon zaben wasu gundumomi da yanzu haka ta tattara, kwana daya bayan gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3pgIA
Niger Wahlen Unabhängige Wahlkommission (CENI)
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Tun dai da yammacin jiya Lahadi ne, jim kadan bayan kammala kada kuri'u a mafi yawancin runhunan zabe a Jamhuriyar Nijar, aka fara kidayar kuri'un da aka kada. Hukumar zabe ta CENI a tsakiyar dare ranar Lahadi ta fara sanar da sakamakon zaben wasu gundumomi da ta tattara. Kawo yanzu dai dan takarar jam'iya mai mulki ta PNDS Bazoum Mohamed ne ke kan gaba da kuri'u a iya yankunan da aka sanar.

Nan da 'yan kwanaki kalilan ne ake sa ran samun cikakken sakamakon zaben da ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, illa dai dan abin da ba a rasa ba da kuma yanki Tillaberi da aka samu hasarar rayuka bayan da wata motar malam zabe ta taka nakiya.

Haka zalika hukumar zaben ta tabbatar da kame wasu bata gari dauke da kuri'un bogi a wasu sassan kasar ta Nijar.