1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cimma yarjejeniyar warware rikicin Tigray

Zainab Mohammed Abubakar
November 2, 2022

Bangarorin da ke yakar juna tsawon shekaru biyu a Ethiopiya sun cimma sulhu, bayan tattaunawar da tarayyar Afirka ta shiga tsakani a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4Iz1K
Pretoria | Waffenstillstandsabkommen für Äthiopien
Hoto: Themba Hadebe/AP/picture alliance

Gwamnatin Ethiopiya da wakilan Tigray sun amince da kwance damarar yaki, kana sannu a hankali kuma cikin doka da oda a tsara yadda za a karbi makamai daga hannun mayakan a cewar manzo tarayyar Afrika (AU) na musammam kuma tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.

Cimma yarjejeniyar sulhu dai wani babban al'amari ne a rikicin na Ethiopiya, inji shi a taron manema labarai da ya gudanar a birnin Pretoria, bayan zaman tattaunawar da ta dauki tsawon mako guda ana laluuben hanyar kawo karshen wannan rikici, da ya kashe daruruwa daura da koran dubbai daga matsugunnensu.