1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na shirin janye dakarunta daga Nijar

April 20, 2024

Kasar Amirka ta amince da janye dakarunta daga Nijar bayan da gwamnatin soji ta soke jarjejeniyar tsaron da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/4f06w
Amirka na shirin janye dakarunta daga Nijar
Amirka na shirin janye dakarunta daga NijarHoto: AFP

Jami'an kasar Amirka sun ce sun amince da bukatar majalisar mulkin soji ta Nijar na janye dakarunsu fiye da 1,000 daga kasar. Jami'an da suka nemi a sakaya sunansu sun bayyana hakan ne gabanin a fitar da sanarwar a hukumance.

A makon gobe ne dai ake sa ran tawagar Amirkar ta kai ziyara birnin Yammai, a wani mataki da ake ganin za su yi amfani da wannan damar ce wajen shiryawa da kuma tsara yadda dakarun za su fice daga kasar.

Karin bayani: Fara janye dakarun Faransa

Ana dai ganin matakin da aka dade ana tsamanni ya kara bai wa Rasha daman samun karin fada a ji a yankin.

A watan Maris din da ya gabata ne dai, Sojojin da ke mulki a Nijar suka soke yarjejeniyar soji da ke tsakaninsu da Amirka tare da mika bukatar ficewar dakarun kasar.

A karkashin yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla, dakarun Amirka da ke hamada na amfani da jiragen sama marasa matuka wajen yakar kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai a yankin yammacin Afirka.