1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaNijar

Al'umma na alhinin rasuwar wakilin DW Hausa

Gazali Abdou Tasawa ATB
February 20, 2024

Al'umma na nuna alhini a game da rasuwar wakilinmu a Yamai Jamhuriyar Nijar Mahaman Kanta wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Litinin a birnin Damagaram.

https://p.dw.com/p/4ccCU
Mahaman Kanta
Mahaman KantaHoto: DW/T.Mösch

Jama'a da dama da suka hada da 'yan siyasa da 'yan jarida da 'yan uwa da abokan arziki na baiyana yadda suka ji da wannan rashi da kuma abubuwan da suke iya tunawa a game da rayuwar marigayi Mahaman Kanta a aikinsa na jarida.

'Yan Nijar da dama musamman ma'abota sauraron gidan radiyon Muryar Jamus suka shiga jimami na rashin wannan shahararren dan jarida wanda shi ne wakili na farko na gidan radiyon DW a Nijar, shekaru sama 30. Alhaji Yahouza Sadissou Madobi, tsohon ma'aikacin DW kana dan siyasa kuma tsohon minista ya bayyana rasuwar Alhaji Mamman Kanta a matsayin babban rashi.

Shahararrun 'yan jarida kamar Alhaji Issoufou Mamane na radiyo Amfani, tsohon ma'aikacin tashar VOA ya bayyana marigayi Mamman Kanta da cewa malaminsu ne a aiki jarida tun a zamnin garmaho

Alhaji Dudu Rahama dan siyasa a Nijar wanda kuma garin su daya da marigayin ya ce Mahaman Kanta ya taka wajen ci gaban siyasarsa da kuma kyakkyawar mu'amalarsa da jama'a.

Malam Chaibou Lili- Goure kane ne kuma amini ga marigayi Alhaji Mahaman Kanta ya kuma bayyana shi a matsayin mutum mai san zumunci da tausayin yara da marayu.

Watanni biyar kenan da Alhaji Mahaman Kanta wanda ya share shekaru da dama yana aika wa DW rahotanni daga birnin Yamai ya koma birnin Damagaram tare da iyalinsa inda kuma a can ne Allah ya yi masa rasuwa.