1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta kama hanyar wargajewa a cewar masana

December 5, 2023

Tsawon watanni da suka wuce, rikici tsakanin bangarori sojoji biyu a Sudan na kashe- kashe, ya kai wani matsayi na durkushewar lamura da tagaiyarar al'umma a cewar kwararru.

https://p.dw.com/p/4Znpp
Sudan Khartum Bürgerkrieg
Hoto: Wang Hao/Xinhua/IMAGO

An dai ruwaito laifukan yaki da kashe-kashe da tagaiyarar al'umma a tsawon watanni takwas da aka yi ana rikicin a Sudan kuma manazarta da dama suna tambayar ko kasar ta kama hanyar zaman marina ko kuma ta kama hanyar wargajewa ne. Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince ya kawo karshen rundunarsa ta musamman  UNITAMS gwamnatin Sudan dai ta bukaci kawo karshen zaman rundunar saboda ta gaza cimma biyan bukata. A  shekarar 2020 aka kafa rundunar domin taimaka wa shirin Sudan na komawa kan tafarkin dimokaradiyya  bayan nasarar matsin lambar sojoji da zanga-zangar 'yan farar hula da suka tilasta wa gwamnatin Omar al Bashir sauka daga karagar mulki. Hager Ali ta  cibiyar nazarin binciken al'amuran kasa  da kasa da ke nan Jamus GIGA ta yi tsokaci da cewa: "Ta ce wannan wani rikici ne da ba a san da shi a baya ba. Ko da yake an taba ganin irinsa a wasu  wurare, amma ba za ka iya cewa ga abin da zai faru  a gaba ba. Ko da ma  wajen shawarin sulhu ne babu wani abu takamamme da za a iya madogara da shi na baya ba. Hatta a cikin  Sudan ita kanta wannan wani abu  ne sabo".

Ficewar rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD a Sudan ya kara dagula al'amura

DRK Truppen aus dem Südsudan landen in Goma
Hoto: Glody Murhabazi/AFP

Manyan kungiyoyi biyu na soji a cikin Sudan,sojojin gwamnatin Sudan da kuma rundunar sa kai ta RSF sun shafe lokaci tun  watan Afirilu suna dauki ba dadi da juna. Rundunar sojin gwamnati na da sojoji kimanin  200,000 karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan yayin da aka yi kiyasin rundunar sa kai ta RSF na sojoji tsakanin 70,000  zuwa dubu dari daya da kuma ke karkashin jagorancin Mohammed Hamdan da aka fi sani da Hemedti. RSF ta aiki ne kamar yan sunkuru lamarin da Hager Ali ta ce ya sanya rikicin zama mai sarkakiya. " Ta ce wani babban abun la'akari shi ne ko wannan rikici zai rikide zuwa irin yanayin rikicin Libya, yadda kowane bangaren zai ja gefe ya kafa gwamnatinsa. A nan ne inda suka banbanta, saboda lokacin da  sojojin gwamnati suka suka matsa zuwa Port Sudan, sun tafi da yawancin hukumomin gwamnati inda suke kokarin kafa sansanoni a can."

Dakarun rundunar RSF na aikata laifukan cin zarafin bil Adama

Mohamed Hamdan Daglo jagoran 'yan tawayen Sudan
Mohamed Hamdan Daglo jagoran 'yan tawayen SudanHoto: Rapid Support Forces/AFP

Kungiyoyin kare  hakkin dan Adam dai tun cikin watan Nuwamba sun ruwaito laifukan cin zarafi da dama da dakarun RSF suka aikata da suka hada da kisa da fyade da fashi da makami. A watan Nuwamba jama'a fararen tsakanin 800 zuwa 2,000 aka kashe a dauki ba dadi wasu 8,000 kuma suka tagaiyara yayin da wasu  da dama kuma suka yi gudun hijira zuwa kasar Chadi. Will Carter Jami'in kungiyar kula da 'yan gudun hijira na kasar Norway ya ce a yanzu babu wata kyakkyawar makoma ga kasar. "Ya ce a zahirin gaskiya wannan wani yanayi ne mai sarkakakiya, muna dai shirin tunkarar  lamura ko da za su rinchabe a shekara mai zuwa. Ba a fidda tsamanin aukuwar annobar yunwa ba, akwai munanan ta'asa da aiaka aikata kuma babu wasu kwararan matakai da aka dauka na shawo kan su. Sabanin wasu rikice-rikice, wannan babbar kasa ce, ana maganar miliyoyin mutanen ninkin yawan jama'ar Syria a saboda haka mutanen suna da yawa kuma kudaden gudanar da  ayyukan tallafi sun yi karanci  a saboda haka aikin ya yi rauni."

Sudan ta rabu gida biyu tsakanin gwamnatoci biyu

Abdul Fattah Al-Burhan da Mohamed Hamdan Dagalo
Abdul Fattah Al-Burhan da Mohamed Hamdan DagaloHoto: Bandar Algaloud/Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Wasu manazarta dai na ganin fadan da ake yi a yanzu na iya raba Sudan gida biyu yayin da wasu kuma ke ganin cewa kasar na cigaba da kasancewa a yanayi na kiki-kaka. Babu dai bangaren da ya nuna alamar sassauci don kawo karshen rikicin tsakanin rundunar sa kai ta RSF da kuma sojin gwamnatin Sudan SAF.