1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Cutar daji ko sankara na kisa a Afirka

Martina Schwikowski BAZ/LMJ
February 4, 2022

Adadin masu dauke da cutar daji ko sankara, na karuwa a yankin Kudu da Saharar Afirka. Masana kiwon lafiya na ganin rashin wayar da kan al'umma, na daga cikin dalilan karuwar.

https://p.dw.com/p/46Xgu
Afirka | Nairobi | Zanga-zangar adawa da matakn kiwon lafiya
Al'ummar kasar Kenya, sun gudanar da zanga-zangar bukatar gwamnati ta dauki matakiHoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

An dai ware ranar hudu ga watan Fabarairun ko wace shekara domin yaki da cutar ta sankara ko kuma daji, ta hanyart fadakar da al'umma. Sai dai ana samun karuwar masu kamuwa da cutar ta sankara ko kuma daji a Afirka, musamman a yankin Kudu da Sahara. Misali a Tanzaniya da ke da yawan al'umma kimanin miliyan 60, yawan likitocin da suka kware a fannin sankara ko dajin a kasar bai wuce 20 ba. Baya ga mtsalar karancin kwararrun likitocin kan cutar da sankara ko daji, asibitoci uku ne kacal ake da su domin masu dauke da cutar kuma cikin ukun biyu ne kawai ke da kayan aiki. Sai dai ana shirin bude cibiyar kula da masu dauke da cutar a Moshi, amma har yanzu babu isasshen kudin samar da cibiyar.

Afirka | Daki da kayan aikin kula da masu cutar sankara ko daji
Ana fama da karancin kayan aiki da kula da masu cutar sankara ko daji a AfirkaHoto: Ashraf Shazly/AFP/Getty Images

Masana kiwon lafiyar dai sun nunar da cewa, kaso 30 cikin 100 na masua dauke da cutar a yankin na Kudu da Saharar Afirka, sun kamu ne sakamakon kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka. Nau'in cutar sankara ko kuma dajin da aka fi kamuwa da ita dai, ita ce ta bakin mahaifa. Haka kuma sun nunar da cewa ana iya yada cutar ta hanyar yin jima'i barkatai ba tare da kariya ba, sai dai babban abin damuwar shi ne mutane ba su da masaniya kasancewar an fi karfafa batun kamuwa da cuta ta hanyar saduwa a Afirka kan cutar HIV/AIDs ko kuma SIDA. Cikin binciken wani shiri kan cutar ta sankara ko daji a duni TCGA, ya nunar da cewa cutar sankara ko dajin bakin mahaifa ce ta fi haddasa asarar rayuka a mafi yawan kasashen yankin Kudu da Saharar Afirkan a shekara ta 2018.

Kiwon Lafiya | Sankara ko dajin bakin mahaifa
Sankarar bakin mahaifa, na yin kisa sosai Hoto: Nora Tam/imago images/ZUMA Wire

Ga misali wani nazari a kasar Tunusiya, bincike ya nunar da cewa adadin wadanda suka rasu sakamakon sankarar ko dajin bakin mahaifar na da yawan gaske. Wani bincike da aka gudanar ya nunar dacewa sama da kaso 75 na wadanda suka kamu da cutar sankara ko dajin bakin mahaifar a 2018, a kasashen yankin gabashi da Tsakiya da kuma yammacin Afirka ba su rayu ba. Koda yake adadin wadanda ke rasa rayukansu sakamkon cutar ya ragu a yankin kudancin Afirka a baya-bayan nan, amma ya karu a baki daya sauran yankunan Afirkan cikin shekaru hudun da suka gabata. Duk da cewa akwai allurar-rigakafin cutar sankarar ko dajin bakin mahaifa, sai dai masana na ganin cewa akwai dari-dari sosai kan yin riga-kafin. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO dai, ta nunar da fargabar yiwuwar karuwa masu dauke da cutar tsakanin shekarun 2018 zuwa 2040.