1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka a Jaridun Jamus 29.03.2024

Abdullahi Tanko Bala M. Ahiwa
March 29, 2024

A wannan makon jaridun na Jamus da dama sun yi sharhi kan zaben Senegal inda aka zabi Bassirou Diomaye Faye.

https://p.dw.com/p/4eFkd
Shugaba mai jirgan gado a kasar Senegal,  Bassirou Diomaye Faye
Zababben shugaban Senegal, Bassirou Diomaye FayeHoto: Luc Gnago/REUTERS

Jaridar die tageszeitung ta ce sabon shugaban Bassirou Diomaye Faye mai shekaru 44 da haihuwa ya kafa tarihi, inda ya kasance mafi karancin shekaru kuma shugaba na biyar da zai jagoranci kasar ta yammacin Afirka mai yawan jama'a miliyan goma sha takwas; da kuma zai maye gurbin shugaba mai barin gado Macky Sall wanda ya shafe shekaru 12 a karagar mulki.

Jaridar ta ce abin da wasu kasashe suka so su yi ta hanyar juyin mulki, shi al'ummar Senegal suka yi ta hanyar kada kuri'a a akwatin zabe. Sabon zababben shugaban Bassirou Faye ya bayyana nasararsa da cewa nasara ce ta Senegal baki daya da za ta tsaya da kafafunta a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Sabon shugaban wanda ya sami gagarumin goyon bayan al'ummar Senegal, ya yi alkawarin tsayawa tsayin daka wajen 'yantar da kasar daga gyauron mulkin mallaka yana mai cin alwashin daidaita rabon arzikin kasa da ma yi wa  kasar garanbawul.

Jaridar ta ce tuni shugaba mai jiran gado Bassirou Diomaye Faye ya nuna alkiblar da gwamnatinsa za mayar da hankali na hadin kan kasa da yaki da cin hanci da rashawa.

Wasu daga cikin wadanda rikicin Sudan ya tagayyara
Wasu daga cikin wadanda rikicin Sudan ya tagayyara Hoto: AFP

Jaridar die Tagesspiegel ta yi tsokaci ne a kan kwasar ganima da lalata kayan tarihi a Sudan sakamakon yaki. Jaridar ta ce tun watan Afrilun 2023 kasar ke fama da yakin basasa tsakanin sojojin gwamnati da rundunar sa kai ta RSF. Bangarorin biyu sun tafka mummunan barna. Miliyoyin mutane sun tagayyara. Harkokin lafiya sun durkushe yayin da aka tilasta wa mutane kimanin miliyan takwas yin kaura daga muhallansu, ga kuma tsananin yunwa da suke fuskanta. Jaridar ta ce a wannan hali babu wanda ke maganar halin da kayan tarihi ke ciki. Jaridar ta ce kayan tarihin Fir'auna an lalata su. Hukumar ilimi da kimiyya da kayan tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta yi kira ga bangarorin su tabbatar da bin dokokin kasa da kasa da alkinta daddadun kayan tarihin da kasar ta mallaka.

Dakarun Putin a Afirka, wannan shi ne taken sharhin Jaridar Sonntagzeitung.

Jaridar ta ce burin sojojin hayar Rasha na Wagner shi ne fadada tasirinsu a nahiyar Afirka kuma wannan kudiri har yanzu yana nan daram duk da mutuwar shugaban rundunar.

Wasu sojojin hayan Rasha na Wagner a Afirka
Wasu sojojin hayan Rasha na Wagner a AfirkaHoto: French Army/AP/picture alliance

Jaridar ta ce tsawon lokaci rundunar ke aiki bisa muradun Vladimir Putin.  Ga shugaban na Rasha Afirka ya fi bai wa fifiko. Tuni ma dai ya gudanar da taron koli har sau biyu da shugabannin nahiyar, da farko a 2019 sannan na biyun kuma 2023. Putin ya rika gabatar da kansa a matsayin shugaban da ya damu da al'amuran kasashe matalauta yana kuma nuna adawa da sabon salon mulkin mallaka na kasashen yamma. Ta haka sannu a hankali ya ke samun tagomashi a kasashen Afirka wadanda suka kosa da iyayen gijinsu na mulkin mallaka a cewar jaridar.