1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta shirya tsaf don fara gasar AFCON

Abdullahi Tanko Bala
January 9, 2022

Bayan shekaru 50 Kamaru na karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta AFCON inda ta ke fatan sake daukar kafin a karo na shida. Sai dai kasar na fatan annobar corona ba za ta dakushe armashin wasannin ba

https://p.dw.com/p/45JNf
Africa Cup of Nations 2021 | Cameroon
Hoto: imago images

Gwamnatin Kamaru ta sanar da kammala dukkan shirye shiryen karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka AFCON ta 2021.

A gasar farko Kamaru mai masaukin baki za ta kara da Burkina Faso a birnin Yaounde. 

Kungiyar Indomitable Lions ta Kamaru wadda ta zo ta biyu a gasar a 2013 na fatan daukar kofin a bana.

Sai dai za su fuskanci zakaru kungiyoyi da suka hada da Algeria da Sadio Mane na Senegal da kuma Mohammed Salah na Masar.