1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damuwa kan sakamakon zabe a Adamawa

February 26, 2023

Al'ummar jihar Adamawa da ke Tarayyar Najeriya, na nuna damuwa kan jinkirin da ake samu game da sakamakon zaben da suka gudanar a jiya Asabar.

https://p.dw.com/p/4O0EA
Najeriya | Zabe | 2023
Har yanzu ba a kammala tattara sakamakon zaben Najeriya baHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Jihar ta Adamwa dai na da kananan hukumomi 21 da kuma mazabu 226, ita ce mahaifar dan takarar babbar jam'iyyar adawa a Najeriyar PDP wato Atiku Abubakar. Sai dai Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, ta danganta jinkirin da ake samu da matsalolin zirga-zirga da ma kasantuwar wasu yankuna da ke musu wuyar kai wa da komowar kayan aikin zabe. Jinkirin dai ya janyo wasu na tunanin cewa, zai iya shafar ingancin sakamakon da ake jiran samu. Matsalar rashin fitowar sakamon dai na ci gaba da daukar hankali ne, ganin yadda hukumar ta INEC ta ce za ta yi amfani da fasahar sadarwar zamani wajen saukaka ayyukanta da dama a wannan karon. Ya zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai kan lokacin da za a kai, kafin a sanar da sakamakon zaben a hukumance.